HOTUNA: Yadda wata Budurwa ƴar Najeriya tayi wuff da wani Bature Tsoho
Wata budurwa ƴar Najeriya ta yi martani ga masu cewa ta auri wani tsoho saboda shi bature ne.
Hakan na zuwa ne bayan ta saka wani hoton bidiyo da ke nuna mijinta jim kaɗan bayan aurensu na gargajiya
Wani ya yi nuni da cewa budurwar ta zaɓi ta auri bature duk da ya girme ta, amma ba ta yarda ba.
Wata budurwa ƴar Najeriya da ta auri wani bature ta garzaya manhajar TikTok domin ta nuna shi ga mabiyanta.
Sai dai, wasu masu amfani da TikTok sun nuna cewa mutumin ya girmi budurwa nesa ba kusa ba, wanda hakan bai yi mata daɗi ba.
Budurwa yar Najeriya ta auri bature
Budurwar ta caccaki masu cewa ta auri .
A wani martani da ta yi cikin wani sabon bidiyo, budurwar mai suna Nkeiruka ta gaya wa mutanen da ke sukanta cewa su je su nemo na su mazajen auren.
Nkeiruka ta ce ta samu nasarar samun mijin nata ta kuma yi wa masu caccakarta martanin cewa su ma su je su nemo na su wanda suke ganin ya cancanta.
Bidiyoyin da ta sanya a TikTok sun nuna cewa budurwar da baturen mijin nata sun yi auren gargajiya ne.
Views: 24
