Labarin Matar da take saida Ruwan Jarka a kura domin ciyar da marayun ta 6 a Kano
Gambo Haruna, wata bazawara wacce mijinta ya mutu shekaru shida da suka wuce, tana fadi tashi don kula da yaransu guda shida
Rahotanni sun tabbatar da cewar matar na siyar da ruwa a baro domin kula da rayuwar yaranta.
Ta ce tana samun kamar N750 zuwa N1,000 a kullun, wanda baya isarta siyan koda sinkin babban biredi guda daya
Ungogo, Kano – Rahotanni sun tabbatar da cewar wata mata mai matsakaicin shekaru wacce mijinta ya mutu shekaru shida sakamakon rashin lafiya, Gambo Haruna, tana fama da matsin rayuwa.
An rahoto cewa ta shafe tsawon shekaru biyu tana sana’ar tura ruwa a baro domin kula da yaranta guda shida.
Tana rayuwa ne a cikin wani gidan laka a Gadar Katako, da ke yankin Rimin Kebe na karamar hukumar Ungogo da ke jihar Kano, wanda take biyan kudin haya N12,000 duk shekara.
Wannan kalubale na rayuwa da take fuskanta ya sa ta tsufa da kuruciyarta, amma duk da haka tana fadi tashi don ganin ta shawo kansu ba tare da ta fada harkar bara ko abubuwan da bai dace ba.
Ta yi bayanin halin da take ciki, cewa tana aiki ba ji ba gani a matsayin mai ruwa don ciyar da iyalinta.
Ta ce a baya ta yi aiki a matsayin lebura a wani kamfani sannan ta dogara da abincin sadaka. Ta ce ta jajirce wajen tura yaranta makaranta, don tana ganin ilimi shine tikitin samun rayuwa mai inganci.
Mijinta ya yi aiki a matsayin karamin ma’aikaci da gwamnatin jihar amma ya rasa aikinsa a gwamnatin da ta gabata.
Daga baya ya yi sana’ar tuka babur kafin gwamnati ta haramta irin wadannan ayyuka, kuma a karshe ya rasu sakamakon karancin jini.
Views: 44
