Ƴan Fashin Daji sun kashe wannan matar saboda taƙi yarda suyi lalata da ita

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Wani mazaunin Jibia a jihar Katsina, mai suna Aminu Yusuf, ya bayyana yadda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da matarsa mai suna Ladi da ke shayar da jariri, suka kuma yi mata auren dole da ɗaya daga cikin waɗanda suka sace ta, inda daga karshe suka kashe ta saboda ta ki amincewa da su su kwanta da ita.

A wani fai fan murya da ya karaɗe shafukan yanar gizo, wata hira ta wayar tarho da aka nada tsakanin Yusuf da shugaban ‘yan fashin.

Jaridar Taskar Labarai ta jiyo tattaunawar shugaban ‘yan fashin yana ba da labarin yadda daya daga cikin yaran nasa wanda ya yi kaurin suna wajen garkuwa da mutane a yankin na Jibia.

Views: 86

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *