Abubuwa ukku da ke saurin kashe soyayya koda ta gaskiya ce

Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Masoya sun bayyana wasu kalmomi wadanda matukar saurayi da budurwa suka rika amfani da su a tsakaninsu to babu shakka zasu iya kawo karshen rayuwar soyayyar su ga kalmomin kamar haka.

1. Zagi: dan kana son son soyayyar ku ta dore kaida masoyiyarka to kar ka rika zagin iyayenta domin hakan yana saurin kawo karshen soyayya ko wace iri ce, duk kuwa da cewa akwai wasu yanmata wadanda ko dukan mahaifansu za kayi ba zasu iya rabuwa da kai ba saboda tsabar kaunar da suke yi maka.

2. Kulawa: kulawa tana daya daga cikin ginshikan soyayya wadda za’a iya cewa ma tana kan gaba, rashinta kuma yana kashe ko wace irin soyayya.

3. Karya: tana daya daga cikin abubuwan da yan mata da samari ke amfani da ita wajen burge junansu amma kuma itama yinta na haifar da matsalolin da ke sanadiyyar mutuwar soyayya.

Views: 272

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *