Almajiran Abduljabbar sun janye labarin rashin lafiyarsa

Almajuran Sheakh Abduljabbar Sheakh Nasiru Kabbara sunyi mi’ara koma baya inda suka janye labarin da suka buga na cewa yana fama da rashin lafiya kuma yana cikin mawuyacin hali.

Bayan yan awowi da buga labarin sun bara suna musanta rashin lafiyar malamin inda suka ce yana cikin koshin lafiya ga abinda suka ce.

Maulanah Sheikh Abduljabbar Kabara(H), yana cikin koshin lafiya bisa kulawar jami’an tsaro.

Ana kira ga dukkan masoya, suyi watsi da duk wata jita-jita da take yawo da take nuna akasin haka.

Labari ne mara tushe, kuma ana jan hankalin yan uwa da su dinga bincike don tabbatar da gaskiyar magana kafin su yada ta.

Allah ya kara kulawa da Amirul Wa’iziyna, ya bayyana gaskiyarsa ya bashi kariya albarkar Ahlul kisa.

~As’habul Kahfi Nigeria Media (AKNM).
22rd July, 2021.

Views: 4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *