An ƙwace Naira Miliyan 3 da aka ba ɗalibar da ta samu maki 362 a UTME an gano cewa na bogi ne

TASHIN HANKALI: Bayan Ta Zana Jarrabawa Ta Samu Tallafin Naira Miliyan Uku Aka Gano Cewa Sakamakon Na Bogi Ne, Aka Janye Tallafin

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire ta (JAMB) ta ce ta janye sakamakon jarrabawar da Miss Ejikeme Joy Mmesoma ta yi na jarabawar Unified Tertiary Matriculation Examination (UTME)

A wata sanarwa da shugaban hulda da jama’a na hukumar Fabian Benjamin ya fitar a ranar Lahadi 2 ga watan Yuli, ta ce Mmesoma ta samu maki 249 a jarabawar sabanin 362 da take yi ikirari.

Kungiyar ta ce za ta gurfanar da Miss Ejikeme a gaban kuliya bisa laifin damfara da sakamakonta na jarabawar.

Ya kara da cewa, Miss Ejikeme ta samu tallafin Naira miliyan 3 daga wanda ya kafa Innoson Motors, Innocent Chukwuma saboda ta samu maki 362 a 2023 UTME.

Sanarwar ta karanta “An jawo hankalin Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Jami’a (JAMB) zuwa wallafe-wallafe da dama a cikin littattafai da kafafen yada labarai na yanar gizo da ke murnar wasu dalibai da suka yi gagarumar nasara a jarabawar UTME ta 2023.

Babban abin tausayi a ciki shi ne batun Miss Ejikeme Joy Mmesoma, wacce ta yi ikirarin cewa ta samu maki 362 a 2023 UTME kuma Cif (Dr.) Innocent Chukwuma ya ba ta kyautar N3m.

Har ma gwamnatin jihar Anambra ta shirya karrama ta a lokacin da daya daga cikin manyan jami’anta ya yi kira ga hukumar JAMB don tabbatar da ikirarinta sai dai hukumar ta bayyana cewa Miss Ejikeme Joy Mmesoma ta samu maki 249 ne kacal ba 362 ba.

Ta yi amfani da sakamakonta na UTME ta yaudari jama’a domin samun guraben karatu (Scholarship) da sauran su.”

Daga Baba Waziri

Views: 24

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *