“Wannan Sana’ata Ce Ta Tsawon Shekaru 4” – Wata Mai Kiwon Kaji Ta Fashe Da kuka Bayan Mutuwar Kajinta 100
Wata mata mai kiwon kaji mai suna Ella Ada ta fashe da kuka bayan tayi asarar kaji har 100 a gonarta.
A shafinta na TikTok ta wallafa bidiyon nata tana kuka saboda asarar dabbobinta.
A cikin faifan bidiyon da ake watsaw a kan Tiktok, matar ta koka kan mutuwar dabbobin da ta ce ba ta da isassun jarin da za ta sake ci gaba da sana’arta a take.
A cewarta, ta yi imanin cewa mutuwar dabbobin nata ba al’ada ba ce, domin ta bar su cikin yanayi mai kyau a ranar.
Ta kara da cewa ta yi imanin cewa wani ne ya saka wa kajinta guba sukaci.
Ta kara da cewa ta shafe shekaru 4 tana sanar kuma mafi yawan dabbobin da ta yi asara basu wuce 10 ba.
Daga Baba Waziri
Views: 37
