A wani zaman da suka yi a jihar Kaduna, shugannin kungiyar Arewa, sun gargadi al’ummar arewacin kasar nan za su kauracewa tafi tafiye zuwa kudancin kasar nan domin tsira da rayukansu sakamakon rikice rikicen da suke ta faruwa a yankin kudancin kasar.
Bayan kammala taron nasu shugabannin sun ce suna bada shawara ga duk wani dan asalin arewacin kasar nan da ke rayuwa a yankin kudu, ya gaggauta tattaro ina shi ina shi ya dawo gida arewa don tsira da rayuwarsa, sannan suna bada shawara ga masu shirin tafiya zuwa kudun domin neman kudi ko wani kasuwanci da su dakata tukunna har kura ta lafa.
Yanzu haka dai ana ci gaba da samun tashe tashen hankula, a wasu sassan kudancin kasar masu alaka da kabilanci ko addini.
Views: 40
