An samu hargitsi a masallacin Juma’a saboda hudubar Liman kan zaɓen su Tinubu a Katsina
An samu wata ƴan hatsaniya a masallacin Kandahar dake cikin garin Katsina jim kadan kafin kabbara sallar juma’a saboda hudubar Liman kan zaɓen da za’a gudanar na shugaban kasa.
Kamar yadda Katsina Post ta samu, Limamin Masallacin, Malam Suleiman Rahama ne dai ya ja Sallah a masallacin.
Kamar yadda majiyoyin Katsina Post da dama suka tabbatar, Liman Suleiman Rahama din ya gabatar da huduba kamar yadda ya saba amma daga karshe bayan ya kammala sai ya kawo maganar zaɓen shugaban kasa da za’a gudanar.
Liman din ya bayyana cewa dukkan manyan ƴan takarar shugabancin ƙasar su uku (3) musulmi ne amma dai akwai wanda ya dauki musulmi a matsayin mataimaki.
Liman din ya cigaba da cewa a matsayin su kuma na kungiyar Izala, shugabannin su a matakin jiha da kasa duka sun tattauna kan mas’alar kuma sun ga cewar shi wanda ya ɗauki musulmi a matsayin matakin shi za su goya ma baya.
Views: 13
