Ankama masu siyar da gawar mutane

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane biyar da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne da suka kware wajen tono gawarwaki daga kaburbura da cire sassan jikinsu domin gudanar da ibada a jihar Ogun.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi a ranar Lahadi ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne a ranar Asabar, 11 ga Maris, 2023.

A cewar kakakin ‘yan sandan, wadanda ake zargin sune; Oshole Fayemi mai shekaru 60, Oseni Adesanya, 39, Ismaila Seidu, 30, Oseni Oluwasegun, 69 da Lawal Olaiya, 50.

An kama su ne biyo bayan wani rahoto da ya jagoranci jami’in ‘yan sanda reshen Odogbolu, Godwin Idehai tare da mutanensa zuwa maboyar su jim kadan kafin su fara wani girbin sassan jikin mutane a garin Ososa.

Oyeyemi ya ce wadanda ake zargin sun amsa cewa suna cikin harkar tono gawarwaki daga kaburbura.

“Sun ce galibi suna sayar da sassan jikin da aka tono ga abokan cinikinsu da ke amfani da su wajen yin ibadar kudi,” in ji PRO na ‘yan sanda wanda ya kara da cewa kwamishinan ‘yan sanda Frank Mba ya ba da umarnin mika wadanda ake zargin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar. domin ci gaba da bincike da kuma gurfanar da su gaban kotu.

Views: 22

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *