Babban bankin Najeriya CBN ya sanar da ƙara wa’adin daina karɓar tsofaffin kuɗi zuwa 10 ga watan Fabirairu.
Gwamnan babban bankinGodwin Emefiele ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.
Gwamnan ya ce ya zuwa yanzu CBN ya karɓi naira tiriliyan 1.9 na tsofaffin kuɗi, saura kuma naira biliyan 900 ya kammala karɓar tsofaffin kuɗaɗe.
Ya yi bayanin cewa sai da CBN ya nemi sahalewar Shugaba Muhammadu Buhari domin ɗage wa’adin karɓar tsofaffin kuɗin, wanda kuma ya amince a ƙara wa’adin da kwanaki 10.
Views: 26
