
Wani Babban limami a kasar Ghana ya bada gudunmawar gina babban coci a ƙasar.
Babban limamin Ghana, Sheikh Osman Sharubutu ya ba da sama da dala dubu takwas a matsayin gudunmawar ginin wani babban coci a ƙasar.
Ginin da ake sa ran za a kammala a 2024, zai kunshi wani wurin adana kayan tarihi na bible da kuma dakin taro mai cin kujeru dubu biyar.
Ghana na da tarihin rashin jituwa tsakanin addinai, ko da yake wannan gudunmawa bai zo da mamaki ba.
Limamin mai shekaru 102 a duniya ya ce ya yanke shawarar yin haka ne domin sake gyara da inganta alaƙa tsakanin Kiristoci da Musulmi.
Ya kuma sha cewa a kullum fatansa shi ne tabbatar da zaman lafiya tsakanin kowanne bangare na addinan ƙasar.
Ko shekaru biyu da suka gabata, sai da ya halarci wani taron kiristoci a coci, batun da ya haifar da ce–ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
©Nasara
Views: 37
