Babu abin kwaɗanta wa mutane a Musulunci Screenshot ɗin abinda Aisha Yesufu ta ce

Aisha Yesufu

Kalaman da shahararriyar mai gwagwarmayar kare haƙƙin mata da yara ƙanana kuma ɗaya daga cikin jaruman matan da suka shige gaba wajen gudanar da taron gangamin EndSARS ɗinnan mai suna Aisha Yesufu.

Wacce ake yiwa laƙabi da macce mai kamar maza, tayi akan addinin Musulunci da Musulmi a ranar 7 ga watan Oktoban daya gabata suna ci gaba da tada ƙura ga dai hoton Screenshot ɗin rubutun nata nan daga ƙasa.

Aisha Yesufu dai ta yiwa addinin musulunci da ƴan uwanta musulmai wankin babban bargo inda tace.

Abu kadan anya musulmace?

Ba musulma bace ba.

Ki daina sa hijabi.

Munafukan banza munafukan wofi ga musuluncin ku a kasa.

Banda talauci, da yaudara, da danne hakin yara da mata me kuka sa gaba?

Ina abun kwadanta ma mutane musulunci?

Kashe kashen?

Fyaden?

Zubar da yara a titi?

Yan mata masu talla?

Cin amanar?

Rashin kula da marayu?

Aikin bar in ji tusa.

A NUNA MANA ZAHIRI A KASA

In ji Aisha Yesufu kamar yadda ta bayyana a shafinta na facebook. ƙarin bayani 👉https://bit.ly/3VgEyHf

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *