Bazan sake Aure ba har’abada—ƴar Najeriya tayi dana sanin Aurenta
Wata matashiya ta sa mutane tofa albarkacin bakunansu a soshiyal midiya bayan ta koka kan kalubalen da take fuskanta a gidan aurenta
Matashiyar mai suna Bella ta sharbi kuka da hawaye yayin da take nuna bakin ciki cewa bata san haka aure yake ba
Bella ta sha alwashin cewa ba za ta sake aure ba a rayuwarta, lamarin da ya jefa mutane cikin halin kaduwa
Cike da hawaye, wata matar aure mai suna Bella ta fadama jama’a cewa abubuwa basa tafiya daidai a gidan aurenta.
Matashiyar ta yi wata wallafa a shafin TikTok inda aka gano ta cikin hawaye shame-shame dauke da taken, ” Ba zan sake aure ba a rayuwata.”
Matashiya tana sharban kuka da hawaye
“Ba Zan Sake Aure Ba a Rayuwata”: Yar Najeriya Ta Koka, Ta Yi Danasanin Aurenta.
Bella ta ce bata taba tsammanin rayuwar aurenta zai shiga halin da yake ciki a yanzu ba. Sai dai kuma bata fito fili ta bayyana menene matsalar da take fuskanta ba.
Wallafar tata ya yi fice a manhajar ta TikTok, inda mutane da dama ke kokarin karfafa mata gwiwa inda suka kawo mata misalai da rayuwar aurensu.
Wasu na mamakin me ya sa har ta shiga wannan yanayi mai tsuma zuciya.
Kalli wallafarta a NAN:
Source:legit.ng
Views: 34
