VIDEO: Tsoho ɗan shekara 70 yayi wuff da budurwa ƴar shekara 15

VIDEO: Tsoho ɗan shekara 70 yayi wuff da budurwa ƴar shekara 15

Jama’a sun yi cece-kuce bayan cin karo da bidiyon wani mutum mai shekaru da ya yi wuff da wata kyakkyawar budurwa.

An dai gano angon wanda ya cika da farin ciki yana cire lullubin da aka yi wa amaryar tasa wanda ke nuna ana budar kai ne
Sai dai mutane da dama suna ganin sam wannan hadin bai yi daidai ba ga tazakarar shekaru da ke tsakaninsu.

Jama’a a soshiyal midiya sun tofa albarkacin bakunansu bayan cin karo da hoto da bidiyon wasu ma’aurata sabbin aure.

Tazarar shekaru da ke tsakanin sabbin ma’auratan shine abun da ya fi jan hankalin jama’a zuwa wurinsu inda sam wannan al’amari bai yi wa wasu dadi ba.

Yadda Hoto Da Bidiyon Wani Ango Da Amaryarsa Suka Ta Da Kura a

A cikin bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya kuma shafin hausaa_fulanii ya wallafa a Instagram ya nuno inda ango ke bude kan amaryarsa cike da farin ciki da zumudi.

Mutane da dama sun ce a ganin farko da suka yi wa hoton, sun zata uba ne da ‘yarsa suke bankwana yayin da za a kaita dakin aurenta sai dai labari ya sha banban duba ga yanayin abubuwan da suka faru a bidiyon.

Ga hoto da bidiyon a kasa:

Source: legit.ng

Views: 28

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *