BIDIYO: “Yadda wani Zobe yaƙi shiga Yatsan Ango ana tsaka da ɗaurin Aure
An sha kallo a lokacin da ake bikin daurin auren wani mutum da amaryarsa a yanayi mai daukar hankali
Sulut Soja a kafar TikTok, ya yada wani gajeren bidiyo da ke nuna yadda zoben angon ya ki shiga yatsansa.
Zoben da aka kawo wa amarya da angon a wurin daurin auren ya yi kankanta ga babban yatsan angon, lamarin da ya jawo cece-kuce
Hotunan bikin daurin aure mai ban mamaki na amarya da ango mai ban dariya ya haifar da martani a kafar TikTok.
An yi dirama a lokacin da mutane suka taru don shaida daurin auren sai kawai zoben ango a ki shiga yatsarsa.
An ga hakan ne a cikin wani bidiyon da Sulut Soja ya yada a kafar TikTok, lamarin da ya ja hankali.
Auren da zobe ya ki shiga ya girgiza intanet
Yadda aka daura, zobe ya ki shiga | Hoto: @user0754576007 Asali: TikTok
Bidiyo ya nuna lokacin da zoben ango ya ki shiga yatsarsa
Da alama zoben daurin auren ya yi kankanta ga yatsarsa ne wanda ke nuna kamar ba a gwada ba kafin halartar wurin bikin.
Bayan shan faman saka zoben cikin yatsar angonta, sai kawai amaryar ta fusata ta fizge daga hannun angon.
Haka dai wasu mutane a wurin bikin suka yi kokarin taya su soka zoben, amma kokarinsu ya ci tura.
Daga karshe dai aka hakura, aka bar batun zobe a rabi-da-rabi har aka daura auren tunda an gama shiri.
Views: 46
