An Cafke Wani Dan Kasar Senegal a Lokacin da Yake Kokarin Dabawa Imam Wuka Yayin Sallar Idi

A wani alamri da ya jefa al’umma cikin fargaba, an dauki bidiyon wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba a wani faifan bidiyo da ya yi yunkurin dabawa wani limami wuka a lokacin da ake gudanar da Sallar Idi.
Rahotanni sun ce lamarin ya afku ne a kasar Senegal yayin da Limamin ya jagoranci mabiya addinin Musulunci wajen gudanar da sallah.
Shaidun gani da ido sun ba da labarin lokacin da mutumin da ba a san ko wanene ba ya bayyana ba zato ba tsammani,nan da nan sai ya tunkari Imam da wuka a hannunsa.
Saurin juyowa limamin ya yi ya ba shi damar guje wa harin ta hanyar tsalle da sauri daga kan tabarmar sallah, da kyar ya guje wa mutumin da zai iya halaka.
Mutane masu jaruntaka daga cikin ma sallatan sun shiga tsakani, inda suka cafke maharin kafin ya ƙara yin lahani.
Daga Baba Waziri
Views: 57
