Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyar APC Bola Tunubu yace canjin sabbin takardun kuɗi da tsadar man fetur an ƙirƙire su ne don yin zagon ƙasa ga zaɓen 2023 inda kuma yace duk tsiyar Buhari sai ya zama shugaban ƙasa.
A wani labarin kuma
A bayalsa Yan sanda sun sami nasarar kame wanda ya kashe budurwarsa:
Hukumomin ‘yan sandan jihar Bayelsa, sun tabbatar da kama wanda ya kashe budurwar tashin wani mutum da ake zargin ya kashe budurwar mai shekaru 22.
A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Asinim Butswat, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin,
Mutumin da ake zargin ya aikata laifin kisa, mai suna Arepamowei Koru, dan kabilar Ogobiri a karamar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa, ya lakada wa budurwarsa ‘yar shekara 22, Miss Toma Serve-god Angolo dukan tsiya har lahira a gidansu ranar Talata.
an Sami hatsaniya tsakanin masoya biyu wanda ya kai ga kisan kai ‘yar uwar wadda aka kashe ɗin ta yi ta ihu na neman temako tare da rike mai laifin kada ya tsere.
Mun samu labarin cewa masoyan biyu an ce suna zaune ne a unguwar ɗaya kafin faruwar lamarin. Mazauna unguwar sun shaidawa DAILY POST cewa, masoyan biyu sun zauna tare ba tare da an samu wani sabani a tsakanin su ba, kafin ƴar karamar rashin jituwar ta shiga tsakanin su a ranar Talata da ta kai ga kisa.
A cewarsu, mutanan anguwar mutumin ya yi mata duka a wani bangare na jiki mai hadari wanda ya kai ga zubar jini kafin mutuwar yarinyar.
“Sun kuma ce taimakon ‘yar uwar marigayiyar ce ta samu nasarar cafke mai laifin kafin ta sanar da ‘yan sanda a sashin Amassoma, domin su kama shi.
Mahaifin marigayiyar, Mista Servegod Angolo, ya garzaya da ita Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Yenagoa, amma rai ya yi halinsa kafin isar su asibiti.
Views: 17
