Buhari ya yi Allah wadai da harin da yan bindiga suka kai wa ƴan sa kai a jihar Katsina

Shugaban kasa Buhari ya yi martani a kan mummunan harin da yan bindiga suka kaiwa yan sa-kai a jiharsa ta Katsina.

Yan bindiga sun kai harin kwauton bauna kan yan sa-kai a yayin da suka bi sahunsu don kwato shanu da dabbobin da suka sace
Da yake mika ta’aziyyarsa ga yan uwan mamatan, Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwarsu ga garuruwansu ba.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da mummunan harin da yan bindiga suka kai wa yan sa-kai a dajin Yargoje da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Wasu yan bindiga sun kai harin kautan bauna kan ayarin yan sa-kai a dajein yayin da suka je kwato dabbobin da maharan suka sace, lamarin da ya kai ga kisa, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Ba za a manta sadaukarwar wadannan jarumai ba, Buhari

Shugaban kasar a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu ya saki a ranar Lahadi, 5 ga watan Fabrairu, ya yi ta’aziyya ga dukkanin yan sa-kai da yan uwan wadanda suka mutu a harin.

Shugaba Buhari ya ce ba za a taba mantawa da sadaukarwar jaruman mazan ba wadanda ke aiki ba ji ba gani don hana aikata laifuka da hukunta masu yinsa a garuruwansu, rahoton The Nation.

Buhari ya yi wa mamatan addu’a inda ya ce:

“Tunaninmu da addu’o’inmu na tare da yan uwan mamatan a wannan mawuyacin lokaci. Allah ya ji kan wadanda suka rasun.”
Harin kwauton bauna: Yan ta’adda sun kashe yan sa-kai a dajin Katsina
A baya mun ji cewa an yi arangama tsakanin yan ta’adda da kungiyar tsaro ta yan sa-kai a jihar Katsina lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla guda 41.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da faruwar al’amarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Isah ya ce yan sa-kai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan maharan da nufin karbo shanu da suka sace. Sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta’addan suka musu harin kwaton bauna.

Source: Legit.ng

Views: 5

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *