Daga yanzu da wanda yayi Digree da mai HND duk matsayinsu daya—Majalissar Dattawa

Majalisar Dattawan Najeriya ta dai-dai ta bambamcin da ke a kwai tsakanin Digiri da HND domin bawa masu kwalin HND damar samun mataki iri daya da na mai kwalin digiri.

Majalissar Dattawan Nijeriya ta sanya hannu akan kudurin da zai dai-dai ta bambamci tsakanin mai digirin farko da masu karatun babbar Difiloma wato HND.

Kudurin wanda kwamitin Majalissar na bangaren manyan makarantu da kuma TETFund suga gabatar wa Majalissar, ya samu nasarar tsallake karatu na daya Dana biyu dana uku, inda a yau Majalisar ta sanya mashi hannu.

Wannan cigaba zai baiwa Masu kwalin HND damar fara aikin Gwamnati daga mataki na 8 har ya zuwa mataki na goma 16, wannan mataki na majalissar bai zo ma wasu da mamaki ba kasancewar dama an dade ana jiran ganin wannan rana.

Menene ra’ayoyinku dangane da wannan batu?

Views: 23

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *