Ku latsa nan don kallon Bidiyon nan

Shahararrinya jarumar fina finan Hausa na Kannywood Maryam Booth ta bayyana cewa darektochi sun daina sakani a Fim, Babu abin da zan zaba, Aure kawai zanyi na zauna a gidan mijina
Fitacciyar jarumar Kannywood Maryam Booth, wacce mahaifiyarta Allah ya yi mata rasuwa a kwanan nan Zainab Booth ta shaidawa kafafen yaɗa labarai dalilin da yasa masu shirya fina-finai (Producers) suka daina sakata a cikin fina-funan su.
Jarumar ta alaƙanta hakan da bayyanar bidiyon tsiraicinta a shekarun baya kamar yadda Neptune Prime ta ruwaito.
“Tun ina ƙarama na kasance ina fitowa a fina-finan Kannywood, saboda mahaifiyata Hajiya Zainab Booth(Allah ya saka mata da gidan Aljanna) ta daɗe a cikin masana’antar, don haka ban taba daina fitowa a fina-finai haka kawai ba.
Amma tunda wani matashi da ake ƙira Dezeel wanda ya yi ikirarin cewa saurayina ne ya bayyana hotunan tsiraici na a kafafen sada zumunta, yanzu mutane na yi min kallon ƴar isaka mara tarbiyya”. In ji ta.
Maryam Booth wadda Hausa Daily Times ta gano a yanzu haka ta koma Babban Birnin Tarayya Abuja da zama tare da ƙaninta Amude Booth tun bayan rasuwan mahaifiyar su, ta ce a duk lokacin da mutane suka ganta yanzu a cikin gari sai su yi ta nuna ta suna ƙiranta da karuwa ko mace mara kunya.
Jarumar ta koka kan yadda alaƙa ta yi tsami tsakaninta da wasu abokan sana’arta da a da suke da matuƙar shaƙƙuwa, a yanzu babu abin da ya rage mata da za ta zaba da ya wuce yin aure a matsayin haryar samun zaman lafiyar da za ta zauna a gidan mijinta.
Masu karatu wane fata zaku yi mata?
Views: 82

Fatan alheri gareki sarauniyar Yan mata hakuri maganin zaman duniya gaskiyane dama hakan rayuwa take kuma shi kome mukaddarine daga Allah s.w.a.yin auren shine mafita gareki Allah ya baki miji nagari ameen summa ameen, kikasace cikin kwanciyar hankali da lumana
Ina yiwa Maryam booth fatan Allah yakawo mata miji Nagari da gaggawa tayi aure ta hutawa rayuwar ta fatan alkhaeri gareki
Mash Allah a ni nawa shawarar kidaure kiyi aure domin shine abu mafi mahimmanci gare a halin yanzu kuma shine hanyar da zaa manta da wannan suna da ake kiranki dashi
Allah ya shiryamu shirin addin in musulunci alfarmar annabi da Qur’ani
Allah yasa hakan shine mafi alkairi kuma inayi maki fatan alkairi dakuma samun mutumin kirki yarone kamar ni
Gaskiya inamiki fatan alkhari dawannan tinanin dakikayi inamik fatan samin miji nagari Allah qarashir yarmu gabakidayanmu
To Maryam ni Ina Miki fatan ALLAH ya Baki miji, Kuma Dan an daina saki a film ba dole sai sana’ar zakiyi ba, ga sana’o’i kala kala. ALLAH ya sa mu dace.