Farfesa Makari ya janye karar da ya shigar a kan Dr Abdallah Gadon Kaya

Wasu rahotanni sun nuna cewa Sheikh Makari ya janye karar da ya shigar akan Dr Abdallah Gadon Kaya kamar yadda jaridar Legit ta ruwaito ga rahoton jaridar Ligit din.

Farfesa kuma malamin addinin Islama, limamin masallacin kasa dake babban birnin tarayya, Abuja, Farfesa Ibrahim Makari, ya bayyana janye karar da ya shigar kan Dr Abdallah Gadon Kaya dake jihar Kano kan zargin ya bata masa suna.

Malamin ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo da Legit Hausa ta samo a yayin wani karatu da yake gabatarwa, inda ya bayyana dalla-dalla dalilan da yasa ya janye karar.

Idan zaku iya tunawa, Makari ya shigar da kara ne, inda ya nemi kotu ta bi kadunsa bisa wasu maganganu da Gadon Kaya ya furta akansa, wadanda Makari ya dangantasu da bata suna.

Bayan da aka kai takardar kara ga Dr Gadon Kaya, malamin ya ce wasu manya a Najeriya, kuma masu fada a ji sun jawo hankalinsa, kuma sun nemi lallai ya janye karar.

“Manya a kasar nan, sun shigo sun nemi, su a bar musu shari’ar. Ma’ana su za su yi shari’ar kar a yi a kotu. Kuma cikinsu akwai shugaban hukumar tsaro na kasa gaba daya, da wasu. Na fada musu cewar zan sanar sunce ba laifi in sanar…

Saboda haka, dalilin haka sun ce su a barsu za su nemi wannan mutumin da yayi maganganu ya fito da hujjar da yace yana dashi su ya basu hujjar.

“Kuma abin ya shafi har iyaye har da mahaifina duk sun amince a kan hakan, sun zabi hakan.

©Legit.comHausa

Views: 96

2 thoughts on “Farfesa Makari ya janye karar da ya shigar a kan Dr Abdallah Gadon Kaya

Leave a Reply to Sanusi Marafa Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *