Faty Gombe matashiyar ƴar fim ɗin da ta fi ko wacce ƴar fim samun yawan sarautu a yankunan Arewa

Hajiya Faty Gombe matashiyar ‘Yar fim ɗin da ta fi kowacce ‘yar fim samun yawan sarautu a yankunan Arewa.

Daga Zaharaddeen Gandu

Matashiyar ‘yar fim ɗin mai suna Hajiya Faty Gombe, wadda tai fim ɗin Rumaisa da kuma fim ɗin Tsumagiya.

Jarumai dai ‘yar asalin jihar Gombe ce, wadda ke da Sarauta 7, inda wadda za a ƙara yi mata a jihar Bauchi 8 kenan.

Ya zuwa yanzu ‘yar fim ɗin ita ce ke da Sarautar; Sarauniyar Mawaƙan Arewa, Zinariyar Mawaƙan Gombe, Zinariyar Doma, Sarauniyar Gabukka, Al-kyabbar Pantami, Gimbiyar Raɓar-bara, Zabiyar Baburawa.

Har wa yau, ‘yar fim ɗin ta ƙara samun wata Sarauta a jihar Bauchi, inda za a yi mata naɗin Sarautar Tauraruwar Mawaƙan Arewa a ranar Asabar 11/02/2023 a cikin jihar Bauchi.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *