Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa mai zaman kanta, wato (ICPC), ta kama wata ma’aikaciyar banki bisa laifin zagon kasa.
Daga Hilal Haruna Malumfashi
A ci gaba da ƙoƙarin an daƙile wasu abubuwan da ke kawo cikas ga kokarin ganin jama’a sun sauya fasalin kudin Naira. Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta ICPC, ta cafke wata jami’ar ɗaya daga cikin bankunan kasuwanci bisa zargin ƙin saka kuɗi a na’urar ATM, bayan kuma akwai kuɗin a bankin
Jami’ar bankin, wacce ita ce shugabar ma’aikata ta bankin Stanbic IBTC reshen Deidei, Abuja, an tsare ta ne saboda da gangan ta ki saka kuɗi a cikin na’urar tantan ce kudi ta (ATM), ga kuma mutane sun yin layi a bakin na’urar ATMs.
A lokacin da tawagar masu sa ido ta ICPC suka mamaye bankin da misalin karfe 1:30 na rana don tabbatar da bin ka’ida, kuma suka bukaci a yi bayani kan dalilin da ya sa duk na’urorin ATM din ba sa ba da kudi, shugaban aiyuka na reshen ya sanar da cewa bankin ya samu kudin ne kawai domin bayar wa ta hanyar musayar hannu da hannu.
Sai dai bayanan da jami’an ICPC suka samu sun nuna cewa reshen ya karbi kudin ne da misalin karfe 11:58 na safe kuma da gangan ya ki saka kuɗin a na’urar ATM ɗin.
Dangane da wannan al’amari ne, kungiyar ICPC ta tilasta wa bankin da ya dora wa na’urar sababbin kudin da aka yi wa gyaran fuska, tare da tabbatar da cewa duk wanda yazo karɓar kuɗi ya samu.
Ana ci gaba da gudanar da bincike, kuma hukumar za ta dauki matakin da ya dace da zarar an kammala su.
Source by ICPC Nigeria.
Views: 6
