Mun yi kuskure wajen canjin kuɗi saboda haka muna neman gafarar ƴan Najeriya—Buhari

Buhari Ya Roki ‘Yan Najeriya Su Bashi Kwana 7 Zai Magance Matsalar Ƙarancin Kuɗi

Shugaba buhari ya bayyana haka ne bayan ganawar su da wasu gwamnonin jam’iyyar APC yau a babban birnin tarayya Abuja.

Ya ce sake fasalin kudin zai kara habaka tattalin arzikin kasar tare da samar da fa’idodi tare da samun jituwa da bankunan.

Haka zalika ya kara da cewa ya ga rahotannin a gidajen talabijin na karancin kudade da wahalhalu ga ‘yan kasuwa da kuma talakawan Nigeria.

Shugaba Buhari ya kuma ba da tabbacin cewa za a yi amfani da kwanaki goman da aka kara na daina karban tsoffin kudaden.

Acikin Kwanaki bakwai zanyi amfani dasu wajen dakile duk wani abin da ya kawo cikas wa talakawan Nigeria, sannan kuma tabbas zamu zartar da hukunci cikin kwanaki bakwai dana roki ‘yan Nigeria.

Daga karshe Gomnonin sun shaida wa Shugaban kasar cewa, a matsayin su na shugabannin gwamnati da na jam’iyya a jihohin su daban-daban, suna cikin damuwa game da tabarbarewar tattalin arziki da zabukan da aka fuskan ta.

Haka zalika Sun bukaci shugaban kasar da ya yi amfani da karfin ikonsa wajen ba da umarni a ci gaba da bunkasa sabbin kudade da tsofaffin takardun har zuwa karshen shekara.

Views: 12

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *