Mawaƙin Amurka ya mutu yana tsaka da cashewa
Fitaccen mawakin Amurka Milton Powell wanda aka fi sani da Big Pokey ya mutu
Mawakin mai shekaru 45 a duniya ya yanke jiki ya fadi yayin da yake tsaka da cashewa a wani gidan giya a yankin Beaumont da ke Jihar Texas a ranar Asabar.
Na’urori sun nuna yadda mawakin ke rike da makirho a hannunsa yake rera waka kafin daga bisani ya yanke jiki ya fadi.
An tabbatar da lamarin a shafin Instagram na mawakin.
“Cikin dimuwa muna sanar da rasuwar dan uwanamu Big Pokey.
“Big Pokey ya rasu. ‘Yan uwansa, abokansa, masoyansa na matukar son shi. Nan da ‘yan kwanaki za mu bayar da bayanai game da bikin birne shi don bai wa mutane dama yi masa bankwana.”
source: hausa.leardership.ng
from opera news
Views: 89
