
A yammacin ranar juma’a ne mai girma gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya je fadar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari inda suka yi ganawar sirri.
A tsakanin su, bayan ganawar kuma aka riƙa samun wasu rahotanni daga ƙarƙashin ƙasa cewa, gwamnan ya je fadar shugaban kasar ne.
Don neman shugaban ya sa baki game da rikicin cikin gida da ke faruwa a jam’iyyar su ta APC, duk da cewa wasu na ganin cewa ba haka lamarin yake ba.
Kawai ya je ne domin neman shugaban kasar ya shiga tsakaninsa da tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso,domin ya sasanta tsakaninsu su.
Views: 42
