Wani gidan mai dake kan titin Aule a Akure, babban birnin jihar Ondo ya tashi da wuta da yammacin ranar Litinin.
Gobarar ta tashi ne a daidai lokacin da wata babbar muta ke sauke kaya a wata kasuwa dake kusa da gidan man.
Shaidun gani da ido sun ce gidan man yana tsaka da siyar da man, inda motoci da masu babura suka yi layi don siya kafin tashin gobarar.
Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, ba a ga motar kashe gobara ko jami’ai a wurin ba.
‘Yan Najeriya dai na fama da matsananciyar karancin man fetur inda farashinsa ya tashi zuwa Naira dari biyar kan kowacce lita a wasu wuraren.
Da alama lamarin ya fi kamari a jihar Ondo yayin da wasu masu ababen hawa suka ce suna sayan naira 1000 kan kowace lita.
Source by LagosCityReporters.
Views: 28
