A wannan watan ne gwamnan jihar Rivers Nyeson Ezanwo Wike ya ce zai bayyana ɗan takarar sa na shugaban kasar duk da cewa har yanzu Gwamnan bai fito ƙarara ya bayyana goyon bayansa ga ko wane ɗan takara ba amma dai ana ganin cewa.
Gwamnan jihar ta Rivers Nyeson Ezanwo Wike zai bayya goyon bayan sa ga ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso inda ya ce zai bashi cikakken goyon baya a duk lokacin da yazo gudanar da yaƙin neman zaɓensa a jihar.
Gwamna Wike ya bayya goyon bayan nasa ga Kwankwaso ne a lokacin da ya gayyace shi domin ƙaddamar da wasu ayyukan raya ƙasa da gwamnatin sa tayi a jihar ta Rivers.
A wani labarin kuma.
AN YI FATAN SHIGA ADDININ MUSULUNCI

Ga shahararren dan wasan kwallon kafa na duniya Cristiano Ronaldo wanda ya koma buga wasan kwallon kafa a kungiyar Alnassr na Kasar Saudiyyah
Christano Ronaldo ya kasance dan kwallo wanda ba Musulmi ba amma yana son Musulunci da Musulmai, kuma yana da dabi’a irin ta Musulmai
An tabbatar da cewa baya shan giya, baya neman matan banza, kuma baya zanen tattoo a jikinsa
Ya kasance mai nuna damuwa da tausayawa Musulmin Palasdinawa wanda suke fuskantar musgunawa da cutarwa daga Yahudawan Isra’ila
Ronaldo yana ware miliyoyin dala na Amurka ya bayar tallafi wa Musulmin Palasdinu saboda jin-kan da yake musu tare da tausayawa
Ronaldo yayi amfani da damarsa da daukakar da Allah Ya bashi wajen bayyanawa duniya zaluncin da ake yiwa Musulmai a Palasdinu, wanda hakan ya jawo masa bakin jini daga gurin wasu makiya Musuluncin, har ya rasa wasu damarmaki a fagen tamaula
Sabanin abokin hamayyarsa Messi wanda yake goyon bayan abinda Yahudawan Isra’ila suke yiwa Palasdinawa
Yanzu Ronaldo ya koma Kasar Musulunci Saudiyyah da buga wasa a daidai lokacin da kwallo ke shirin sallamarsa daga yayi, muna fatan hakan ya zama dalilinsa na shiga addinin Musulunci
Yaa Allah Ka dubi bawanKa da idon Rahama, Allah Ka masa tukwici da shiga addinin Musulunci kafin ya bar Saudiyyah
Views: 17
