Zaa fara koyarda yara da yaren uwa a najeriya.
Maaikatar ilmi ta dakatar da koyarwa da yaren turanci a makarantun Firamaren Najeriya.
Wannan ya biyo bayan sabon tsarin da gwamnatin tarayya ta ƙirƙiro, wanda ya wajabta koyarwa da yaren uwa a matakin Firamare.
Hakan na nufin, a jihar Kano, da sauran jihohin da Hausa yafi tasiri, yaren zai zama hanyar koyar da darasi a makarantun.
Ministan ilimi, Adamu Adamu, yace daga matakin ƙaramar Sakandire, za’a riƙa haɗawa da turanci wajen bayar da darasin.
Ana sa ran fara gudanar da wannan sabon tsarin koyarwa nan da farkon shekarar 2023 mai kamawa.
Views: 26
