Tsoho ɗan shekaru 69 yayi targaɗe a garin jibgan ɓarawon kaji a zariya.
Yadda wani dattijon tsoho mai kimanin shekaru 69 ya samu mummunar targaɗe a hannun sa na dama a sakamakon shiga cikin ayarin matasa ana dukan wani ɓarawon kaji da aka cika hannu da shi a birnin Zariya.”
Wakilin mu ya halarci wurin “inda ya kalato mana cewa a yunƙurin ganin yadda fusatattun matasan suka riƙa jibgan ɓarawon tamkar rai zai fita da ƙyar dai aka samu aka ƙwace ɓarawon kajin daga hannun waɗannan matasan shi kuma dattijon aka tafi da shi gidan wanzamai domin duba lafiyar hannun nasa.”
Lamarin ya faru ne a yau talata 17/10/2023 a anguwar ƙarfe dake birnin zariya jihar Kaduna.”
Views: 12
