Wani matashi ya bayyana mummunan halin da ya shiga ranar da ya kwana a gidan Budurwar sa

  • Wani matashi dan Najeriya ya bayyana yanayi mai ban tsoro da ya shiga bayan ya zabi kwana a gidan wata matashiyar budurwa
  • Da tsakar dare, matashin ya ce ya yi mummunan mafarki inda wani aljani ya yi kokarin makure shi
  • Bayan ya bude idanunsa, abun da ya gani ya sanya shi fara addu’a neman tsari kafin karfe 4:00 na asuba

Wani matashi dan Najeriya,

@TheOnlyATM, ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya bayyana halin da ya shiga a lokacin da ya kwana a gidan wata matashiyar budurwa.

@TheOnlyATM, ya bayyana mummunan yanayin da ya shiga bayan wani shahararre a dandalin X, Agba, ya bukaci maza da su bayyana mummunan abun da ya faru da su a ranar da suka kwana a gidan mace.

Matashi da budurwa a daki
Matashi Ya Bayyana Mummunan Yanayin Da Ya Shiga Bayan Ya Kwana a Gidan Budurwa Hoto: Delmaine Donson. An yi amfani da hoton don misali ne kawai Asali: Getty Images

Ya yi mummunan mafarki

Matashin ya ce ya yi mummunan mafarki da tsakar dare. A cikin mafarkin, ya ce ya kasa yin ihu domin wani aljani ya yi kokarin makure shi. @TheOnlyATM ya farka sai kawai ya ga matashiyar tana magana da kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tuna cewa kafafunta sun kasance a saman bango yayin da take magana da kanta. Wannan ya tsorata shi. Mai amfani da dandalin na X ya ce:

“Agba, na ziyarci wata matashiyar budurwa a baya don haka na kwana a wajenta. Da tsakar dare, na yi wani mummunan mafarki, kamar wani aljani na kokarin makure ni kuma na kasa ihu. Don haka sai na bude idona kawai sai na ga matashiyar nan ta sakala kafafunta a saman bango sannan tana magana da kanta. Na kusan karar da jinin Yesu kafin karfe 4 na asuba.”

https://apahausa.com.ng/video-ku-kalli-yadda-%c6%b4an-bindiga-ke-lalata-ta-matan-mutane/

Views: 66

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *