Ku latsa nan don kallon Bidiyon
Wani dan kasuwa mai suna Mallam Umar Tasiu, ya sha bulala har lahira da wasu surukansa suka yi masa a garin Minna na jihar Neja.
Wani makwabcinsa ya shaida wa Daily trust marigayin da ya kammala karatunsa a Jami’ar Alazhar da ke Masar ya je ganin ‘ya’yansa da ke zaune da tsohuwar matarsa a gidan mahaifinta.
“Ya je ya ga ‘ya’yansa guda biyu da suke zaune tare da tsohuwar matarsa a gidan mahaifinta. Sun rabu amma yaran suna wurin mahaifiyarsu. Ya je ya gansu amma surukansa na baya ba su so ya zo gidansu. Bayan isarsa sun daure shi suka yi masa bulala har ya mutu a gidansu.
Views: 50
