Babban Limamin Masallacin Abuja Sheikh Ibrahim Makari Ya Karbi Bakuncin Baƙin Balarabe A Abuja
Shararran Malamin Addinin Musulunci A Najeriya Kuma Babban Limamin Masallacin Abuja Farfesa Ibrahim Makari Ya Karɓi Bakuncin Ibrahim Hamisu Wanda Akafi Sani Da Bakin Balarabe A Gidan Shi Dake Abuja.
A cikin satin nan ne, dai idan baku manta ba Baƙin Balarabe, ya kudurci tafiya zuwa Abuja akan raƙumi domin yi ma Farfesa Ibrahim Makari barka da Shan-ruwa wanda daga bisa ni ya dakatar dashi cewa ya hawo mota ya same shi duba da matsalolin rashin tsaro da ake fama dasu a Najeriya.
A rahoton da “Katsina Reporters ta samu ya tabbatar da cewa Baƙin Balarabe ya samu ƙyakkawar tarba daga Sheikh Ibrahim Makari, inda ya bashi masafki tare da yi mashi rakiya zuwa babbar majalissar ƙasa.
source: katsinareporters
Views: 7
