Hukumar dake kula da rumbun Abinci na gwamnati ta tsaurara tsaro a rumbun ta na Kaduna

Hukumar NEMA ta tsaurara tsaro a rumbun abincin ta na Kaduna

Hukumar NEMA ta bayyana bukatar jami’an tsaro da su taya su gadin dakin ajiyar kayan abinci da suke dashi a jihar Kaduna.Wannan ya biyo bayan fasa dakin ajiyar abinci na NEMA da wasu jama’a suka yi a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas.

‘Yan Najeriya na ci gaba da dandana wahala da zafin cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi kwanan nanJihar Kaduna – Hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta yi kira ga jami’an tsaro na farin kaya (DSS) da ‘yan sanda da kuma rundunar sojojin Najeriya da su tsare ma’ajiyarta a jihar Kaduna.

Kodinetan ofishin NEMA na shiyyar Kaduna, Abbani Imam, wanda ya bayyana hakan, ya danganta lamarin da abin da ya faru a jihar Adamawa.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu jama’a suka kutsa cikin dakin ajiyar NEMA da ke Adamawa tare da wawashe kayan abinci da nufin rage wa kansu radadin cire tallafin man fetur.NEMA na neman tallafin sojoji wjajen kare rumbunta

Views: 59

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *