Idan aka raba Najeriya zamu fi kowa shan walaha—Sarkin Yarabawa

Sarkin Yarabawa a Najeriya, ya bayyana rashin gamsuwarsa da raba Najeriya ya ce idan aka raba Najeriya sai mun fi kowa shan wahala saboda haka bama goyon bayan duk wani mataki na raba kasar nan  – in ji shi.

Sarkin yarbawa a jihar Osun, Abdulrashid Akanbi ya bayyana cewa, idan aka raba Najeriya, yarbawa sai sun fi kowa Shan wuya.

Yace Jihar Legas ce kawai ke iya biyan albashin ma’aikatanta amma duka sauran jihohin sai sun jira kudin gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa, kuma mafi yawan mutanen su ma’aikatan Gwamnati ne, dan haka yace masu neman a raba kasar su daina.

A watannin da suka gabata ne dai wani da ake kira Sunday Inogbo, ya yi ikirarin ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Oduduwa, ta Yarabawa zallah, kafin a murkushe yunkurin na sa, Najeriya dai na ci gaba da fama da masu tayar da kayar baya domin ballewa daga kasar musamman a yankin kudanci.

Views: 17

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *