Yan Najeriya na cigaba da mayar da martani kala kala da kuma bayyana mabambantan ra’ayoyinsu dangane da goge sakon da shugaban kasar Muhammadu Buhari, ya wallafa a shafinsa na kafar sadarwar Twitter, wanda ya jawo ce-ce ku-ce a ciki da wajen kasar.
Wannan mataki na kamfanin ya kuma sa wasu sun fara kiraye kirayen da a toshe kafar Twitter a fadin kasar sakamakon bacin ran da suka ce sun shiga ta sanadiyyar goge sakon shugaban kasar Muhammadu Buhari wanda suke cewa hakan cin fuska ne ga shugaban.

Wannan shine dai sakon da shugaban ya wallafa a shafin nasa da harshen Turanci, sakon yana dauke da kalamai masu tsauri ga masu tayar da kayar baya da kai hare hare a kasar.
Views: 30
