Wallahi idan APC bata tsayar da Sen, Barau a matsayin dan takarar Gwamnan Kano ba sai mun rusa ta—Danbilki

Shahararren gogagge kuma sanannen dan siyasar nan na jihar Kano, Alhaji Abdul’aziz Dan Bilki Kwamanda, ya bayyaba cewa zasu ruguza jam’iyyar APC mai mulkin jihar matukar bata tsayar da gwaninsu Sanata Barau I Jibrin Maliya, a matsayin dan takarar kujerar gwamnan jihar Kano ba a zaben 2023 dan bilki ya ce.

“Wallahi Idan Ba Barau Jibrin Ne Ɗan Takarar Gwamna A Kano Ba, Sai Mun Fasa Bakin Farantin APC, Sai Mun Ruguza ta,” Inji Ɗan Bilki Kwamanda, kawo yanzu dai jam’iyyar ta APC ta fada wani rikicin cikin gida wanda ake ganin babbar illane ga jam’iyyar.

Sai dai waau na ganin jam’iyyar za ta shawo kan wannan rikici tare da dinke barakarta nan ba da jimawa ba.

Views: 21

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *