“Ina da daurin gindin da babu wanda ya isa ya kama ni a kasar nan—Mr Inogbo

Hoton Sunday Inogbo

Masu fafutukar kafa kasar Yarabawa zallah wato Oduduwa Republic, sun ce babu gudu babu ja da baya a yunkurin da suke yi na ballewa daga tarayyar Najeriya, saboda jagoransu Mr Sunday Inogbo ya umarce su da suci gaba da matsawa gwamnatin Najeriya lamba.

Har sai ta amince da bukatunsu ta basu yancin kansu domin kuwa sun gaji da zama a tarayyar Najeriya, idan kuma ba haka ba za su yi duk mai yiwuwa wajen kwatarwa kansu yancin kai daga tarayyar Najeriya ko da tsiya ko da arziki.

Yayin da a bangare guda aka ambato jagoran nasu Mr Sunday Inogbo, yana cewa, shi fa babu yadda za’ayi ya mika wuya domin kuwa sai ya ga abinda ya turewa buzu nadin, kuma yana da daurin gindi saboda haka da hujja yake fafutukarsa kuma babu wanda zai iya kama shi.

Views: 25

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *