Ina roƙon gafarar al’ummar jihar Kaduna su yafemin laifukan da nayi musu—El’rufai

Gov Naseer Elrufa’i

Mai girma Gwamnan jihar Kaduna Malam Naseer Ahmad El’rufai ya nemi gafarar al’ummar jihar ta Kaduna bisa kura kuren daya tafka a kan mulkinsa, ganin cewa ƴan watanni suka rage ya sauka daga mulki.

Daga Shafin Malam Datti

BAUCHI DA GOMBE DAYA NE

‘Yan uwa Gombawa diban fari ku ajiye wukar, ku sanya wa zukatanku ruwan sanyi akan batun rijiyar man fetur dake Kolmani

Kolmani yana kan iyaka da karamar hukumar Alkaleri a jihar Bauchi da kuma Akko a jihar Gombe, wato zamu ce wannan albarka yana tsakanin Bauchi da Gombe ne, shine maganata ta gaskiya

Tabbas da jihar Bauchi da jihar Gombe mallakin Gwamnatin tarayya ne, kuma Gwamnatin tarayya ita ke da iko akan rijiyar man,, don haka jihar Bauchi da Gombe zasu shiga cikin jihohin Nigeria da suka mallaki arzikin man fetur (Oil States) wanda za’a ware musu kaso na musamman kamar yadda yake a tsarin Gwamnatin tarayya

Rijiyoyin man fetur dake Kolmani zai amfani dukkan jihohin tarayyar Nigeria ne ba Gombe da Bauchi ba

Zamu iya yin raha, idan Gombawa sukace Kolmani mallakinsu ne daidai ne, hakanan idan mutanen Bauchi sukace nasu ne daidai ne, domin tabbas yankin Kolmani ya shafi jihar Bauchi da Gombe

Shiyasa lokacin da Maigirma Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya yazo kaddamar da rijiyar man Kolmani, sai da Gwamnan Bauchi da Gwamnan Gombe suka halarta, kuma duk sunyi jawabi, sun tabbatar rijiyar ya shafi jihar Bauchi da Gombe

Ni banga abin fada da cacar baki tsakanin Gombe da Bauchi ba, mu ‘yan uwan juna ne tamkar jini da hanta, sai dai muyi wasa da raha, amma duka arzikin namu ne

Ina alfahari da Bauchi kamar yadda nake alfahari da Gombe, Bauchi da Gombe a gareni duk abu daya ne

Muna rokon Allah Ya albarkaci jihar Bauchi, Gombe da sauran jihohin Arewan Nigeria, Allah Ya sa mu amfana da rijiyar man fetur na Kolmani

Views: 15

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *