Ina so na saki matata ne saboda kyawunta yayi yawa -Wani mutum ya fada wa kotu
Wani mutum ya shaidawa kotu cewa ba ya son matarsa Hilda Mleya, mai shekaru 30 kuma saboda ta yi kyau sosai.
Arnold Masuka, wanda ya shigar da karar, mai shekaru 40, ya yi wannan ikirarin ne a gaban kotun karamar hukumar Lusaka.
A cewar Zambia Observer, Arnold yana saki matarsa ne saboda kyawunta da ke sa shi barci.
Lamarin ya yi muni har yana tsoron zuwa wajen aiki ko ya bar ta ita kadai don yana tsoron kada wasu maza su kwace ta.
Babban magatakarda, Mista Chenjerai Chireya, ya ce wannan ne karon farko da ya fara gudanar da irin wannan lamarin.
Arnold ya yanke shawarar yin amfani da kotu don raba shi da matarsa bayan ya gane cewa ita ce mace mafi kyau da ya taba gani a Gokwe.
Ya shaida wa kotun cewa matarsa tana murmushi a kodayaushe kuma yana fargabar hakan na iya jawo hankalin wani mutum.
Da yake yanke hukunci a kan lamarin, Cif Chireya ya bukaci iyalan biyu da su daidaita batun da ma’auratan.
Views: 15
