
Shahararriyar jarumar Kannywood Ummi Rahab ta sake ɗaukar hankalin mabiyanta a shafin sada zumunta na Twitter.
Bayan rubutan da ta yi a makon daya gabata inda tace, “Samun macce irinta sai namiji mai ƙoƙarin sallar dare.
A jiya ma sai da jarumar ta sake yin wani rubutu da ya ɗauki hankalin mabiyanta a shafin Twitter.
Inda ta ɗora hotonta ɗauke da wata yarinya ta ce “jama’ar Twitter ga ƴata ku sanya mata albarka ni na haifi kayata da kaina” kamar yadda zaku gani daga ƙasa.

Sai dai bayan yin wannan rubutu ta samu mayar da martani daga ɓangaren mabiya shafin nata ga kaɗan daga ciki.

Views: 21
