Jama’a sun caccaki budurwar da ta fusata saboda saurayin ta ya tarbe ta da Doya da Manja

Jama’a sun caccaki budurwar da ta fusata saboda saurayin ta ya bata Doya da Manja

Wata budurwa ta kada kafar sada zumunta bayan da ta yada abincin da aka ba ta lokacin da ta ziyarci wani saurayinta
Budurwar ta ziyarci saurayin nata ne a karon farko zuwa gidansa, inda ya yanke shawarin dafa mata abincin da za ta ci


Sai dai, abin da zai iya ba ta ba komai bane face tafasasshen doya da manya da kuma ruwan leda gama-gari
Wata budurwar ‘yar Najeriya mai suan @nihiinn a Twitter ta yanke shawarin zurfafa alakarta da wani saurayinta, ta ziyarce shi har gida.

Don burge ta, matashin ya zauna, inda ya hada mata abinci mai dadi dafin gida da ba zai yi wahalan samu ba.

Nan take ya dafa doya, ya baje ta da manja kana ya dauko ledar ruwa ya danka ma budurwar. Lokacin da ya ba ta abincin, sai kawai ta gaza ci.

Yadda budurwa ta fusata bayan saurayi ya bata doya da manja
Kalan abincin da saurayi ya ba budurwarsa.


Cikin fushi ta dauki hoto abincin, kana ta yada shi a kafar Twitter don bayyana yadda ta ji game da wannan saurayin nata.

Ta ce:

“Na ziyarci wannan mutumin a karon farko. Ya bani doya da manja da ledar ruwa.”

Sai dai, jama’ar kafar sada zumunta sun caccake ta bisa daukar hoton abincin da saurayin ya bata tare da yada shi a Twitter.

Source:hausa.legit.ng

Views: 32

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *