
Masoya shirin Film ɗin A Duniya mai farin jini na ci gaba da dakon cigaban shirin kashi na 61.
A kwanakin baya dai mashiryin shirin na A Duniya wato Tijjani Asase ya bayyana ɓacin ransa ga ƴan downloading.
Wsɗanda ke sauke shirin a manhajar YouTube suna siyarwa da mutane ba tare da izini ba.
Inda ya koka game da hakan kuma har ya fito da poster yace duk mai sana’ar downloading zai siya domin cigaba da sana’arsa.
Har ma ya bayyana cewa ga duk mai buƙatar kallon film ɗin kafin ma su ɗira shi a shafin YouTube za su suyar masa domin ya kalla.
Kawo yanzu dai kusan makonni biyu kenan ba tare da an saki cigaban shirin Film ɗin ba a shafin YouTube kamar yadda aka saba.
Ga duk mai buƙatar kallon cigaban shirin dai zai iya tuntubar mashiryin shirin Tijjani Asase domin samin shi.
Views: 20
