Rahotanni sun bayyana cewa yayan majalissar dokokin jihar Katsina sun tada kura a zauren majalissar jihar ta Katsina kan matsalar tsaron da ke addabar yankunansu yayin da wasun su ma suka fashe da kuka ku kalli wannna bidiyon don ganin yadda ta kaya.
Mambobin majalisa sun fashe da kuka saboda yawaitar harin ‘yan bindiga
‘Yan majalisar dokokin jihar Katsina biyu, a ranar Litinin, sun fashe da kuka a bayyane bisa yawan hare-haren da aka kai kwanan nan a cikin al’ummomin jihar ta Katsina, The Cable ta ruwaito.
Da yake magana ranar Litinin a zauren majalisar wanda kakakin majalisar Tasi’u Maigari ke jagoranta, Shehu Dalhatu-Tafoki, mataimakin kakakin majalisar, ya gabatar da wani kudiri na “mahimmantar da bukatar jama’a cikin gaggawa” kan matakin rashin tsaro a jihar.
A cewar Dalhatu-Tafoki, mamba mai wakiltar mazabar Faskari, duk da kokarin gwamnatin tarayya da na jihohi, da hukumomin tsaro, har yanzu al’ummomi na fuskantar hare-hare.
Don haka, ya yi kira ga hukumomin gwamnati da abin ya shafa da hukumomin tsaro da su sake wata dabarun.
A kalamansa:
“Akwai matukar bukatar kayan aikin tsaro a cikin jihar ta yadda za su kara yawan wuraren aikin su a fadin jihar, musamman wuraren da abin ya fi shafa.”
“Rundunonin da ke yankunan ba su isa ba. Ba za su iya shawo kan lamarin ‘yan bindiga ba, duk da makudan kudaden da ake kashe musu.”
Ya kuma yi kira ga sauran jama’a da su ci gaba da addu’ar Allah ya dawo da zaman lafiya a fadin jihar.
A cikin gudummawarsa, Haruna Goma, dan majalisa mai wakiltar mazabar Dandume, ya ce an kashe mutane 11 a wani harin baya-bayan nan da aka kai kan al’ummomi biyu a Dandume, yayin da aka sace wasu mazauna da yawa.
A cewar kamfanin dillacin labarai na Najeriya (NAN), yayin da yake ba da labarin abin da ya faru, dan majalisar ya fashe da kuka, sannan ya bukaci gwamnati da ta taimaka wa al’ummomin da abin ya shafa.
Hakazalika, Abubakar Mohammed, mamba mai wakiltar mazabar Funtua, shima ya fashe da kuka yayin da yake ba da labarin yadda ‘yan bindiga ke kai farmaki kan al’ummomi a cikin watan da ya gabata, inda suka kashe mutane da dama tare da yin garkuwa da wasu.
A nasa bangaren, dan majalisa mai wakiltar mazabar Batsari, Jabir Yusuf, ya bayyana kisan mutane 12 da aka yi kwanan nan a Duba, wata unguwa a Batsari, a matsayin abin takaici.
Bayan tattaunawa da ‘yan majalisar, majalisar ta amince da kudirin tare da yin kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su yi kokarin magance matsalar cikin gaggawa ta hanyar tabbatar da tsaro a cikin al’ummomin da abin ya shafa.
Zauren ya kuma yanke shawarar yin taro da ‘yan majalisar tarayya daga Katsina, da kuma gwamnatin jihar, wajen kokarin magance rashin tsaro, in ji rahoton Punch.
Hakazalika zauren ya kara yanke shawarar ganawa da hukumomin tsaro da kwamitin jihar kan tsaro don nemo hanyoyin maido da zaman lafiya a yankunan da ke fuskantar kalubale.
Views: 26
