Ku rubuta ku aje litar man Fetur zata dawo ₦50 a mulkin Tinubu—Fasto Elijah

Litar Man Fetur za ta dawo Naira 50 a Najeriya, inji Fasto Prophet Elijah Bamidele.

Wani babban Malamin coci ya bukaci yan Najeriya su kara hakuri, Tinubu kadai zai iya gyara kasar nan.

Ya ce Litar mai da mutane ke ta wayyo Allah ta kai N617, zata dawo N50 kacal a kasar nan.

Malamin ya bayyana cewa Allah ya gaya masa ‘yan Najeriya zasu yi sharholiya a mulkin Tinubu. Fitaccen Malamin addinin kirista a Najeriya, Prophet Elijah Bamidele, na cocin Christ House of Prayer and Deliverence ya tabbatar da ‘yan Najeriya na shan wahala.

Malamin ya ce baki daya mutanen kasar nan, ko mutum ya zabi shugaba Bola Tinubu ko bai zabe shi ba, yana fama da wahalhalun rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Views: 39

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *