Kwamishinan Kasafin-kuɗi na Zamfara ya yi murabus tare da sauya sheƙa zuwa PDP

Kwamishinan Kasafin-kuɗi na Zamfara ya yi murabus tare da sauya sheƙa zuwa PDP

A yau Juma’a ne Kwamishinan Kasafin Kudi na Jihar Zamfara, Alhaji Aliyu Mafara ya yi murabus da ga mukaminsa, inda ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki, ya koma PDP.

Mafara l, wanda shine Kwamishinan Kasafin Kudi a gwamnatin Gwamna Bello Matawalle, ya bayyana cikakken goyon bayansa ga dan takarar gwamnan PDP a jihar, Dauda Lawal Dare.

Da ya ke magana a yau Juma’a a yayin taron bikin karɓar sa da aka gudanar a gidan dan takarar gwamnan jihar na PDP da ke Gusau, tsohon kwamishinan ya nanata cewa tunanin sa ba zai bar shi ya ci gaba da zama a inda ake ta samun koma-baya ba.

Ya ce, “Na sanar da tsohon gwamnan jihar, Gwamna Abdulaziz Yari, da dukkan magoya bayana kafin ficewata daga APC zuwa PDP.

“Ina yin haka ne domin jama’a, kuma ina da yakinin cewa Dr. Dauda Lawal, idan aka ba shi dama a zabe mai zuwa na mulkin jihar Zamfara, zai magance matsalar tsaro, da bunkasa noma, da samar da kasuwanni masu kyau na noma,”

A nasa bangaren, dan takarar gwamnan jihar Zamfara a karkashin jam’iyyar PDP, Lawal Dare, ya bayyana Zamfara a matsayin jihar PDP, yana mai jaddada cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara a zabe mai zuwa.

Ficewar kwamishinan kasafin kudin na zuwa ne sa’o’i 48 bayan wasu mashawarta na musamman 40 sun fice daga jam’iyyar APC zuwa PDP.

Views: 18

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *