Labarin wani Masunci da ya tsinci Gawar Yaro a komar kamun Kifi
Bayanan hoto, Yayin da ƙasashen Tarayyar Turai ke ɗaukar matakan yaƙi da bakin haure, mutanen da abin ya shafa na ci gaba da kokawa kan wahalar rayuwa da ta sa suke barin ƙasashensu na asali.
Yayin da adadin baƙin-haure da ke yunƙurin shiga Turai ke ƙaruwa, haka ma adadin waɗanda ke mutuwa sanadiyyar hakan a Tekun Baharrum.
A gefe guda kuma, yayin da ƙasashen Tarayyar Turai ke ɗaukar matakan yaƙi da su, mutanen da abin ya shafa na ci gaba da kokawa kan wahalar rayuwa da ta sanya suke barin ƙasashensu na asali, abin da ke zama gagarumar matsala a gaɓar ruwan Tunisiya.
Daidai lokacin da rana ke fitowa a saman tekun da ke gabashin Tunisiya, masunci Oussama Dabbebi ya fara jawo komarsa idanunsa sun yi ƙuri a kan abin da yake janyowa daga ruwan saboda ba kifi kawai ake samu ba a kodayaushe.
“Maimakon kifi, wani zubin nakan samu gawarwaki. Karon farko na firgita, amma a hankali na saba. Daga baya ma dai janyo gawa a komata ya zama kamar kamun kifi.”
Masuncin mai shekara 30 sanye da ‘yar riga da gajeren wando, ya ce a kwanan nan ya janyo gawar ‘yan cirani 15 cikin kwana uku.
“Wata rana na kamo gawar jariri. Wane irin laifi jariri ya yi wa wani? Na yi kuka. Da a ce babba ne to da ɗan sauƙi saboda ya rayu, amma dai jariri, ai bai ga komai ba,” a cewarsa.
Mista Dabbebi ya saba kama kifi a tekunan da ke garin Sfax na Tunisiya tun yana shekara 10 da haihuwa.
A wancan lokaci, yana cikin mutane masu yawa da ke sana’ar kama kfiin, amma ya ce yanzu da yawa sun sayar da jiragensu ga masu safarar mutane zuwa Turai kan farashi mai tsoka.
A lokuta da yawa, masu safara sun sha yi min tayin kuɗi mai yawa don na sayar musu da jirgina. Kodayaushe sai na ƙi yarda, saboda idan aka yi amfani da jirgina kuma wani ya nutse a ruwa, ba zan taɓa yafe wa kaina ba
Views: 24
