Labarin Yadda wani Mutum ya Auri Surukarsa bayan Mutuwar Matar sa

Labarin Yadda wani Mutum ya Auri Surukarsa bayan Mutuwar Matar sa

Wani mutum ya nemi surukarsa mai shekaru 57 ta aure shi bayan matarsa ta mutu tana da shekaru 34

Mutumin mai shekaru 46 ya rasa matarsa bayan ta haifa masa yara uku kuma a yanzu yana shirin sake aure.

Ya ce baya son kawo wata daga waje cikin gidansa, amma wasu na kallon shirinsa na auren uwar matarsa a matsayin haramun

Wani magidanci na neman auren surukarsa (uwar matarsa) shekaru biyu bayan mutuwar matarsa.

A labarin da Azuka Onwuka ya wallafa a Facebook, mutumin ya ce gwanda ya auri mahaifiyar matarsa sannan ya guji kawo wata daga waje.


Wani Mutum Na Shirin Auren Surukarsa Bayan Mutuwar Matarsa

Matar mutumin ta mutu tana da shekaru 34, inda ta bar yara uku, maza biyu da mace daya.

Mutumin wanda yanzu shekarunsa 46 yana neman auren mahaifiyar matarsa wacce ke da shekaru 57 a duniya.

Views: 33

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *