Lalataccen Kirista a kudancin Najeriya yafi Musulmin ƙwarai ɗan Arewa—Kashim Shettima

Lalataccen Kiristan Kudu Ya Fi Musulmin Kwarai Dan Arewa Chanchantar Ya Zama Shugabancin Majalisar Dattawan Najeriya, Inji Kashim Shettima

Daga Comr Abba Sani Pantami

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce ba daidai ba ne musulmin Arewa ya zama shugaban majalisar Dattawa ba.

A yayin wani zaman tattaunawa da Sanatoci a Abuja, Shettima ya ce a shirye ya ke ya durkusa domin rokon Sanatoci masu zuwa da su zabi Godswill Akpabio (APC-Akwa-Ibom) da Sanata Barau Jibrin (APC-Kano) domin ya jagoranci majalisar dattawa ta 10.

Mataimakin Shugaban kasar ya ce: “A shirye nake in durkusa in roki abokan aikina don amfanin kasa, wannan shine cigaban wannan al’umma.

“A nan muna tare da shugaban kasa musulmi kuma mataimakin shugaban kasa musulmi a tsarin kabilanci da addini irin namu.

“Lamba 1, 2; Imani guda daya don Allah! A halin da ake ciki yanzu, mafi munin, kiristan Kudu ya fi Musulmin Arewa mafi tsafta ga Shugabancin Majalisar Dattawa.

Wannan shine wakilinmu a fadar shugaban kasa, Allah ya kyauta.

Allah ka tsaremu daga sharrin son zuciya da har idonmu zai rufe mu fifita lalataccen Ar*ne sama da Musulmi dan uwanmu saboda siyasa.

Shin tun farko Kashim Shettima baisan da tsarin Musulmi da kirista bane a kasar, kuma ya yita bin kafa akan lallai yana Neman Vice President har sai da aka bashi?

Ya kamata mutane su sani kamar yadda aka zabi shugaban kasa da Mataimakin shugaban kasa, haka suma zababbun Sanatoti suke da alhakin zaban nasu shugabannin don haka babu wanda ya isa ya musu dole a barsu gobe Talata su zabi wanda suke so.

Views: 16

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *